Ƙetare
Ya zama wajibi a ƙarshen yaƙin Ukraine ranar 8 ga Agusta- Shugaba Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, ya zama wajibi a samar da yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a ƙarshen wa’adin da ya bayar na ranar 8 ga watan Agusta, a cewar wani babban jami’in diflomasiyya na Amurka.
Jami’in John Kelley ya shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya cewa a shirye Amurka ta ke ta ɗauki wasu matakai domin samar da zaman lafiya, sai dai bai yi ƙarin bayani kan ko waɗanne irin matakai ba ne.
Kalaman sa na zuwa ne bayan harin da Rasha ta kai Kyiv, babban birnin Ukraine da jirage marasa matuƙa waɗanda suka kashe mutane 13 da kuma jikkata wasu 130.
You must be logged in to post a comment Login