Labarai
Ya zama wajibi a kawo ƙarshen barazanar tsaro ga dalibai – Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta kasa NHRC ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan kare dalibai daga barazanar tsaro.
Shugaban ƙungiyar Tony Ojukwu ne ya bayyana hakan a Abuja, gabanin babban taron da ƙungiyar za ta gudanar karo na 4 a ƙasar nan.
Tony Ojukwu ya ce, kai wa makarantu hari tare da kashe dalibai ko sace su babbar barazana ce da za ta haifar da koma baya a bangaren ilimi.
Har ma ya bayyana cewa, taron ƙungiyar na bana zai mayar da hankali kan tattauna batun ƙalubalen tsaro a harkar ilimi, don samar da mafita mai kyau ga yara masu tasowa.
You must be logged in to post a comment Login