Labarai
Ya zama wajibi al’umma su baiwa ilimi fifiko-Dr Bashir Sani
Wani malami a kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi dake nan Kano, Dr Bashir Sani ya ce, ya zama wajibi al’umma su baiwa fannin ilimi fifiko domin shi ne matakin gina rayuwa baki daya.
Dr Bashir sani, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin duniyar mu a yau nan Freedom Radiyo da ya mayar da hankali kan muhimmanci da tasirin da ilimi ke da shi a rayuwar al’umma.
Ya kuma ce abunda ya banbanta dan Adam da dabba shi ne ilimi da tunani, idan aka sami karancin masu ilimi a cikin al’umma to tilas al’umma ta samu koma baya.
A nasa bangaren , tsohon Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar sakandare ta Gwale Malam Ali Sa’adu ya bayyana cewa, sun kafa kungiyar tsofaffin daliban ne domin bunkasa harkar koyo da koyarwa a makarantar ta su.
Shi ma Malam Muhammad Nura Abdullahi, na sashin koyor da addinin musulunci a jami’ar Bayero ta Kano cewa ya yi ya zama wajibi gwamnatoci da al’umma su dauka cewar neman ilimi abu ne da ya zama dole a cikin rayuwar kowane dan Adam.
Ya kara da cewa mafi muhimmancin al’umma ita ce wadda take da ilimi.