Labarai
Ya zama wajibi jama’a su kula da lafiyar dabbobin da za su siya domin layya- Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi al’umma dasu kasance masu tsafta musamman a wannan lokacin bikin sallar layya.
Kwamishinan Lafiya na Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar Lafiya ta Kano Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa fitar a yau Talata.
Sanarwar ta gargadi al’umma da su kiyaye gurbata muhalli ta hanyar inda ya kamata su dinga zubar da dagwalo, domin kare lafiyar su da muhalli.
Kwamishinan ya kara da cewa wajibi ne jama’a su kula da lafiyar dabbobin da za su siya domin layya, inda ya ce akwai wasu dabbobi da suke dauke da cutukan da za su iya yaduwa ga mutane musamman idan ba a kiyaye matakan kariya ba wajen yanka da kuma suya ko dafa wa ba.
Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya kuma yi kira musamman ga iyaye mata da masu dafa abinci da su tabbatar da cewa sun wanke nama da ruwa mai tsafta, da kuma dafa naman sosai, wanda hakan zai taimaka matuka wajen kashe kwayoyin cuta da ke iya kasancewa a jikin naman.
Dakta Labaran ya kara da cewa Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta tanadi isassun magunguna da kayan agajin gaggawa a asibitocin gwamnati, domin bayar da taimakon gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.
Haka kuma, kwamishinan, ya yi fatan al’ummar jihar Kano za su gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali, lafiya da kuma farin ciki.
You must be logged in to post a comment Login