Labarai
Yadda Abdulmumin Kofa ya shirya addu’ar zaman lafiya da yakar Corona a Kano
Fitaccen dan siyasa kuma Babban Daraktan hukumar samar da gidaje ta kasa ya ce Gwamnatin tarayya zata cigaba da shirya tarukan addu’oi na malamai don yiwa kasar nan addu’oi na musamman don neman daukin mahalicci kan barazanar tsaro da yankin Arewacin kasar ke fuskanta a yanzu don kawo karshen matsalar.
Abdulmumin Jibrin Kofa ne ya bayyana hakan a ya yin taron addu’oi na musamman da ya shirya wanda aka tara malamai a karamar hukumar Bebeji don gudanar da addu’oi kan matsalolin dake addabar kasar ciki har da dawowar cutar Corona karo na biyu.
Babban Daraktan hukumar samar da gidaje ta kasa ya kara da cewa an shirya taron ne don neman daukin mahalicci kan matsalolin da Najeriya ke fuskanta na rashin tsaro da kuma sake dawowar cutar Corona karo na biyu har ma da matsalar matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta domin shawo kan matsalar.
Kofa yace a kokarin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi da gwamnatin Kano a kowanne mataki shi ma zai cigaba da bata tasa gudunmawar wajen tallafawa jama’ar Kiru da Bebeji da ma Kano da kasa baki daya musamman ta fuskar tsaro har ma da yunkin dakile yaduwar cutar Korona.
You must be logged in to post a comment Login