Labarai
Yadda ‘yansada suka yi ram da daya daga cikin matasan da ake zargi da yankewa yarinya matunci a Bauchi
An kama daya daga cikin matasan da suka yi wata yarinya aika-aika a Jama’aren jihar Bauchi kafin tawagar gwamnatin jihar ta zo nan Kano a jiya Lahadi.
Hakan yasa muka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi DSP Ahmad Mohammed Wakili.
“Yace tuni hukumar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta baza mutanen ta don nemo wadanda suka aikata wannan ta’asa Kuma yanzu haka sun Sami nasarar kama mutum daya daga ciki mai suna Adamu Abdul’aruf mai kimanin shekaru ashirin”
A cewar DSP Ahmad Mohammed dayan da ake zargin sun aikata wannan mumunan aika-aika ya tsere.
Kuma a jiya Lahadi ne Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya aiko da tawaga ta mussaman da ta wakilci shi zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake nan Kano don ganin halin da yarinyar ke ciki.
Abdulzak Nuhu Zaki kwamishinan kananan hukumomin Jihar Bauchi shi ne ya jagoranci tawagar kuma yace yanzu haka an kama wasu daga cikin wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Hon. Abdulzak Nuhu Zaki yana mai cewa “Gwamnatin Jihar Bauchi ta yi alkawari za ta dauki nauyin biyan kudin aikin da za’a yiwa Hauwa”.
Ana dai zargin wasu matasa biyu da yankewa wata yarinya mai suna Hauwa ‘yar kimanin shekaru shida matancin ta.
Wannan al’amarin ya faru ne a garin Jama’are dake jihar Bauchi a ranar Larabar makon da ya gabata.
Wakiliyar mu Hadiza Ado Jinta da ta ziyarci asibitin Malam Aminu Kano ta zanta da
Hafsatu wadda ita ce marikiyar yarinyar kuma yayar mahaifin yarinyar ta bayyana yadda abun ya faru.
“Ta ce ta dumama ruwan zafi zata yi musu wanka sai suka fita, fitar su ke da wuya sai suka hado da matasan ya yin da suka tambaye ko kun san gidan Suraja daga nan ne suka umarce su da su je wani Kango daga nan ne kuma yar uwar ta ta tsare, bayan nan ne suka kwantar da ita suka yanke Matuncin ta daga aka dauke ta zuwa asibiti”
You must be logged in to post a comment Login