Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda aka yi garkuwa da ‘yar ‘dan majalisar Jiha a Kano

Published

on

A daren ranar Asabar ne wasu masu garkuwa da mutane suka kutsa cikin gidan dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Danbatta, suka sace yar sa suka tafi da ita har yanzu babu duriyar su.

Wasu makusantan dan majalisar sun shaidawa Freedom Radio cewar wannan al’amari ya tayar da hankulan garin matuka musamman ma a wannan lokaci da maganar garkuwa da mutane ta fara lafawa a jihar Kano.

Majiyar tace jami’an tsaro na ta kokarin gano wadannan masu garkuwa da mutane, sai dai har zuwa wannan lokaci babu duriyar su, majiyar tace sun fara samun kiran waya daga mutanen da ake zargin sune masu garkuwar.

Mun tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna wanda yace a bisu bashin wannan bayani zuwa gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!