Labarai
Rahoto: Yadda ake ci gaba da dashen bishiya a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta fara dashen bishiyoyi kimanin miliyan 2 a sassan jihar Kano da nufin magance kwararowar Hamada da zaizayar ƙasa gami da ambaliyar ruwa.
Dashen an fara gudanar da shi a ƙarshen watan Agustan da ya gabata karkashin ma’aikatar muhalli ta jihar kano da nufin taƙaita barazanar da muhalli ke fuskanta a wannan zamani.
Wannan dai ya biyo bayan rahoton da hukumar bada agajin gaggawa NEMA ta fitar a baya bayan nan da ke bayyana hasashen da ta yi game da samun ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomi 20 na jihar Kano.
Hakan ne ya sanya gwamnatin jihar Kano ta mayar da hankali wajen samar da bishiyoyin a sassan jihar Kano don magance matsalar cikin hanzari.
Binciken masana muhalli ya bayyana cewa samar da bishiyoyi yana raje barazanar kwararowar Hamada da zaizayar ƙasa har ma da dakile matsalar ambaliyar ruwa.
To ko mutane sun san muhimmancin dasa bishiya dama matakan da za su dauka don samar da su tare da inganta su? Wasu mutane anan Kano sun bayyana ra’ayoyin su kamar haka.
“Sun bayyana cewa sanin mahimmancin dasa bishiya ya sanya suke dasawa a unguwanni da cikin gida tare da alkinta wanda ake samarwa a kan hanyoyi sun kuma cewa suna sane da mahimmancin dasa bishiya ta wajen bayar da iska mai kyau da jikin dan adam ke bukata”.
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bayyana tasirin da dasa bishiyoyin za su yi ga rayuwar al’umma har ma da muhalli.
“Mun mayar da hanakali wajen dashen bishiyar da za ta samar da katako wanda hakan zai kara habbaka tattalin arzikin”
Dr Kabiru Ibrahim Getso, ya ce gwamnati na dab da ƙaddamar da dokar da za ta hukunta wadanda ke sare bishiyoyi barkatar don kawo ƙarshen matsalar.
You must be logged in to post a comment Login