Labarai
Yadda Badaru ya sanya hannu kan kasafin kudin badi
Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya sanya hannu kan dokar kasafin kudin badi ta 2021, da za’a kashe fiye da Niara biliyan 156.
Muhammad Baduru Abubakar ya ce fiye da kaso Hamsin cikin dari bangarorin ilimi da kiwon lafiya suka samu cikin kasafin kudin badin.
Gwamnan dai ya sanya hanu ne da yammacin wannan rana ta Talata a gidan gwamnatin jihar dake birnin Dutse, jim kadan bayan da Majalisar dokokin jihar ta dawo da kudirin kasafin kudin ga fadar gwamnatin jihar.
A cewar gwamnan taken kasafin kudin badin shi ne ci gaban kasafin kudin ko kuma dorawa ne kan na wannan shekarar mai karewa.
Da yake jawabi shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Idris Garba Jahun ya ce tsarin da gwamnan ya fito da shi ya sanya aka kammala nazirin kasafin kudin ba tare da bata lokaci ba.
Alhaji Idris Garba Jahun ya kara da cewar, ba bu wani abun daka sauya cikin kudirin kasafin kudin kafin ya zama doka, kasancewar an yi masa taza da tsifa.
You must be logged in to post a comment Login