Coronavirus
Yadda cibiyar gwajin Corona ta Dangote ke aiki a Kano

Gidauniyar Dangote ta bayyana cewar, alhakin gwamnatin Kano ne daukar samfurin mutanen da cibiyar zata yiwa gwaji, a sabon dakin gwajin cutuka na zamani da gidauniyar ta bayar kyauta ga gwamnatin Kano wanda zai ringa gwada mutane dubu daya a kowacce rana.
Babbar jami’ar Dangote Foundation Hajiya Maijidda Modibbo ce tayi wannan bayani domin wayar da kan mutane kan yadda katafaren dakin gwajin cutar Korona ke gabatar da aikinsa.
Hajiya Maijidda Modibbo, tace aikin wannan cibiya shine karbar samfurin wadanda za a gwada kai tsaye daga gwamnatin Kano, daga nan kuma idan sun yi gwajin sai su mika sakamakon ga hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC wacce itace zata bayyana sakamakon.
Hoton yayin kaddamar da cibiyar gwajin da gidauniyar Dangote ta samarwa jihar Kano
Gidauniyar Dangote tace ba itace ke da alhakin daukar samfurin wadanda za a yiwa gwajin ba, Haka kuma ba itace da alhakin fitar da sakamako ba, Dan Haka aikin cibiyar bashi da alaka da mutane kai tsaye.
Daga bisani Hajiya Maijidda Modibbo ta bayyana shirin Gidauniyar Dangote na cigaba da tallafawa al’umma da gwamnatin jihar Kano wajen yaki da wannan annoba ta Covid-19.
Hoton yayin kaddamar da cibiyar gwajin da gidauniyar Dangote ta samarwa jihar Kano
Hoton yayin kaddamar da cibiyar gwajin da gidauniyar Dangote ta samarwa jihar Kano
You must be logged in to post a comment Login