Labaran Kano
Yadda cutar Corona Virus ta shafi ‘yan Najeriya a kasar China
Biyo bayan bullar annobar cutar Corona Virus a kasar China ta haifar da sauyin yanayi ga al’ummar kasar ciki har da ‘yan Najeriya mazauna kasar ta China.
Wani Dan Najeriya dake kasar ta China ya bayyana mana cewa a yanzu haka mafi yawan ‘yan Najeriya suna zaune a gida, basa zuwa ko ina, idan ba abinda ya zama tilas ba.
A bangaren dalibai, yanzu haka ana hutun makarantu, amma duk da haka takaita zirga-zirgar daliban musamman wadanda suke zaune a makaranta, sannan an hana shige fice, don gudun yada cutar ga dalibai.
A ranar 15 ga watan Fabrairun da muke ciki ne ake sa ran dalibai zasu koma makaranta a kasar, amma hukumomi sun dage komawa makarantar har sai an ga abunda hali yayi.
Har kawo yanzu, ba’a samu wani dan Najeriya ko nahiyar Africa da ya kamu da cutar ba.
Rahotonni daga kasar ta China na cewa hukumomi sun dauki tsauraran matakai na takaita zirga-zirgar jama’a, da kuma rufe manyan wuraren haduwar jama’a, wadanda suka hadar da kasuwanni da wuraren wasanni da sauran su.
Al’umma na amfani da abin kariya wajen shakar iska wato ‘Mask’ don gudun kamuwa da cutar.
Hukumomin kasar ta China sun samar da wasu layukan wayan hannu da tangarahu na musamman da za’a amfani da shi wajen yin kira don neman agajin gaggawa.
Sannan tuni aka samar da wata manhaja wadda take isar da bayanai kan halin da ake ciki a yaki da cutar ta Corona Virus a kasa, a manhajar dai ta kan kawo bayanan adadin mutanen da suka kamu da cutar a kullum.
Idan zaku iya tunawa dai, cutar ta Corona Virus ta fara bulla ne a yankin Wuhan na kasar China mai yawan al’umma miliyan goma sha daya.