Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Yadda gwamnati ta bankaɗo gidan Mari a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bankaɗo wata makarantar mari a unguwar ƴar Akwa da ke Na’ibawa.

Kwamishinan harkokin addinai Muhammad Tahar Baba Impossible ne ya bayyana hakan, lokacin da ya kai sumame gidan a ranar Alhamis.

“Mun samo rahoto kan yadda ake ɗaure mutane a wannan makaranta, don haka muka ɗauko tawagar mu da jama’an tsaro don mu gani, kuma ga shi mun zo mun tarar da matasa da yara a ɗaure” in ji Baba Impossible.

“Jihar Kano mu ma mun yi biyayya ga umarnin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na haramta gidajen mari a ƙasar nan, don haka babu wanda yake da hurumin sake sanya mutane a mari”.

Kwamishinan ya ce, a yanzu sun samu sama da mutane 47 da ke ɗaure a gidan marin, kuma za su wuce da su don lalubo iyayen su tare da ɗaukan mataki na gaba.

“Bayan mun zo malamin da yake da alhakin kula da makarantar yayi ƙoƙarin musanta cewa shi bai san da makarantar ba, don haka a matsayin mu na gwamnati za mu ɗaukin da ya dace akan laifin da ya aikata”.

Shi ma mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun miƙa malamin zuwa sashin binciken manyan laifuka don faɗaɗa bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!