Coronavirus
Yadda kwamishinan lafiya ya warke daga cutar Corona

Kwamishinan lafiya na jihar Lagos Farfesa Akin Abayomi ya warke daga cutar corona.
Hakan na cikin jawabin da kwamishinan yada labaran jihar Gbenga Omotosho ya fitar a yau Litinin a shafin sa na Twitter.
Tun a ranar 24 ga watan Agustan da muke ciki ne aka sanar da cewa Farfesa Akin Abayomi ya kamu da cutar corona.
Sanarwar ta bayyana cewa tun a jiya Talata gwaji ya tabbatar da cewa Abayomi ya warke daga cutar.
You must be logged in to post a comment Login