Addini
Yadda shari’ar Abduljabbar ta kasance
Kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu karkashin jagorancimn mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ta yanke wa Abduljabbar Nasir Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A zaman kotun na ranar Alhamis, ta tabbatar da kalaman batanci da Abduljabbar ya yi ga ma’aiki SAW a cikin karatunsa.
Yanzu haka dai kotun ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Malam Abduljabbar Kabara, bisa samunsa da laifin yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad S.A.W a karatun da yake gabatarwa a masallatansa.
Haka kuma kotun ta kwace dukkannin litattafansa da ke gaban kotun tare da yin umarnin karbe masallatansa.
Tun da fari dai kotun ta fara da yin karatun baya kan zargin da ake yi wa Abduljabbar Kabara, tare da sake nazartar shari’ar da aka gabatar a baya.
Daga bisani ne kuma kotun ta ce ta same shi dumu-dumu da laifin yin kalaman batanci ga annabi a karatun da yake gabatarwa, sakamakon yadda kotun ta gamsu da hujjojin masu gabatar da kara da kuma shaidun da aka gabatar a kotun, wanda suka tabbatar da Abduljabbar ya yi wadannan kalamai na cin mutuncin ma’aiki.
A don haka mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya ce Abduljabbar ne ya kirkiri kalaman da kansa, domin shaidu da hujjojin da kotu ta karba sun tabbatar da cewa babu su a cikin litattafan da yake fada.
Yayin da ake ci gaba da zaman shari’ar, kotun ta ce laifin da ake zargin Abduljabbar da shi za a yi masa hukunci karkashin sashe na 382 na kundin hukunta manyan laifuka na Penal Code.
Daga nan ne daya daga cikin lauyoyin da ke kare shi Barista Aminu Abubakar ya nemi a yi masa sassauci, saboda kuskuren fahimta ya yi har ta sanya Malam Abduljabbar ya aikata wannan laifi.
Amma nan take Abduljabbar ya miƙe a gaban alkali ya ce ba da yawunsa lauyan yake magana, domin bai ma san shi ba, kuma baya neman sassauci, a don haka ya bukaci kotun da ta gaggauta yi masa hukunci domin zai yi mutuwa ta girma.
A karshe dai bayan tafiya hutun rabin lokaci, kotun ta dawo ta kuma yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Abduljabbar Kabara, bisa tabbatar da laifinsa.
Daga nan ne mai sharia Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya ja hankalin malamai da su rinka tauna abin da za su furta a wajen karatunsu.
Zaman shari’ar da ake yi tsakanin gwamnatin Kano da Malam Abduljabbar kan zargin yin kalaman batanci ga annabi Muhammad S.A.W dai na yau shi ne ya zamo na talatin, kuma wanda aka yanke hukunci a yau.
You must be logged in to post a comment Login