Jigawa
Yadda Sule Lamido ya karbi cin hancin sama da biliyan daya a wajen ‘yan kwangila – EFCC
Wani shaidar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gabatar a shari’ar da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Jigawa alhaji Sule Lamido mai suna Micheal Wetkas, ya bayyana yadda tsohon gwamnan jihar ta Jigawa da ‘ya’yansa biyu da kuma wasu mutane hudu suka rika karbar na goro daga wajen ‘yan kwangila.
A cewar shaidar EFCC mutanen bakwai sun rika amfani da kamfanonin su wajen karbar cin hanci daga wajen ‘yan kwangila da gwamnatin jihar Jigawa ta basu aiki.
Mista Wetkas ya ba da wannan shaidar ne a shari’ar zargin cin hanci da ake yiwa tsohon gwamnan na Jigawa Sule Lamido da ‘ya’yansa, Aminu da Mustapa.
Sauran wadanda ake zargin sune: Aminu Abubakar da kuma Bartholomew Agoha da kuma kamfanonin su biyu wato Bamaina Holdings da kuma Speeds International Limited.
Wadanda ake zargin ana tuhumarsu da aikata laifuka 43 gaban mai shari’a Ijeoma Ojukwu na babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargin damfarar jihar ta Jigawa naira biliyan daya da miliyan talatin da biyar.
You must be logged in to post a comment Login