Labarai
Yadda tankar mai ta kama da wuta a Lagos
Wata tankar mai ta kama da wuta a yankin Magboro da ke babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.
Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe shida na safiyar yau Laraba, bayan da jami’an hukumar kashe gobara suka kai daukin gaggawa.
Motar dai na cikin jerin motocin da suka yi dakon man fetur, ana dai zargin cewa motar ce ta kwace gada hannun direbanta tare da bin hannun da ba nasa ba.
Wannan dai na zuwa kwanaki Ashirin da biyar da fashewar wata tankar mai a yankin “Kara”.
Hukumar kiyaye abkuwar haddura ta kasa ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce mutane biyu ne suka rasa rayukansu tare da konewar ababen hawa 29.
You must be logged in to post a comment Login