Labarai
Yadda Tolulope Arotile ta rasa ranta a Kaduna
Rundunar sojin saman kasar nan ta ce, a karon farko kasar nan ta yi rashin matukiyar jirgin sama a karon farko mai suna Tolulope Arotile sakamakon hatsari mota da ya rutsa da ita a yammacin Talatar da ta gabata a jihar Kaduna.
Hakan na cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar Air Commodore Ibekunle Daramola ya fitar a jiya Talata.
Tolulope dai ta fara aiki a rundunar sojin saman kasar nan ne a watan Satumbar shekara ta dubu biyu da Bakwai, kuma ita ce mace ta farko da da ta fara tuka jirgin shalkawabta.
Sanarwar ta bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar nan ta aike da sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar tare da nuna alhini bisa rashin ta.
You must be logged in to post a comment Login