ilimi
Yajin aiki: ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makwanni 3
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni uku kan ta fara aiwatar da yarjejeniyar da suka suka cimma ko kuma ta tsunduma yajin aiki.
Shugaban ƙungiyar Farfesa Emmanuel Osodoke ne ya sanar da hakan bayan kammala taron shugabannin ƙungiyar na kwanaki biyu a jami’ar birnin tarayya Abuja.
Farfesa Osodoke ya ce a baya can sun janye yajin aikin da suka ƙuduri aniyar shiga bayan alƙawuran da gwamnatin tarayya ta yi na aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma.
Sai dai a yanzu ba su da mafita fa ce shiga yajin aikin da zarar makonni ukun sun cika ba tare da samun biyan buƙata ba.
A bara ne dai ƙungiyar ta gudanar da yajin aikin watanni tara, don nuna rashin jin daɗi kan kin biya mata buƙatunta da gwamnatin tarayya ta yi.
You must be logged in to post a comment Login