Labaran Kano
Yakamata a’lumma su siffanta da dabi’ar kunya-Limamin Zam-zam
Limamin masallacin Juma’a na Zam-Zam karkashin cibiyar addinin musulunci ta Jama’atul Wa’azu wal Irshad dake Hotoro Tsamiyar Boka Malam Muhammad Sani Amin Idris ya ja hankalin al’ummar musulmi wajen siffanta da ta’adar kunya a harkokin su na yau da kullum.
Malam Muhammad Sani Amin Idris wanda na daya daga cikin limamin masallacin Juma’a na Zam-Zam ya bayyana hakan ne yayin Hudubar Sallar Juma’a da ya gabatar.
Ya ce shakka babu dabi’antuwa da kunya kai ya taimakawa wajen kyautata lamura a tsakanin al’umma.
Ya kuma kara da cewa akwai bukatar iyaye da sauran magabata su dage wajen kimsawa ‘ya’yan su dabi’u masu kyau a wani bangare na samar da ingantacciyar al’umma ana gaba.
Mahukunta su mai da hankali kan al’umma -Limami
Limamin jumu’a a Kano yayi Allah-wadai da “Black Friday”
Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito limamin Malam Muhammad Sani Amin Idris ya ce ba a bukatar kunya a abubuwan da suka shafi addini, wanda zata haifar da rashin aikata koyarwar annabin tsira Muhammad (S.A.W).