Labarai
Yaki da hamada: Mun dasa bishiyoyi sama da dubu a Kano – Make Kano Green
Gamayyar matasan Kano da ke gangamin dasa bishiyoyi a Kano da ake kira Make Kano Green sun ce, cikin watanni goma sun shuka bishiyoyi 1,567 a kananan hukumomin biyar daga cikin kananan hukumomin 44 na Kano.
Babban jami’in gangamin Isma’il Auwal ne ya bayyana hakan, a zantawarsa da Freedom Radio a ranar Lahadi yayin da su ke ci gaba da shuka bishiyoyi a yankin Yalwa dake unguwar Mariri.
Isma’il Auwal ya kara da cewa, suna samun hadin kan al’umma wajen gudanar da gangamin dashen bishiyoyin, haka kuma suna bibiyar dukkanin wuraren da suka dasa shuka, domin ganin halin da suke ciki a lokaci bayan lokaci.
Karin labarai:
Ganduje zai dasa Bishiyu miliyan biyu domin kiyaye zaizayar kasa
Canjin yanayi na haifar da kwararowar hamada – Masani
A nasa bangaren mai unguwar ta Yalwa, Alhaji Abdullahi Shehu ya ce, sun yi farin ciki da wannan gangami, sannan ya yi alkawarin yin shiri na musamman domin kula da bishiyoyin da aka dasa wajen ganin basu lalace ba.
Sai dai irin wannan yunkuri da matasan ke yi, na fuskantar barazana, musamman daga masu dabi’ar saran itace, wadanda mafi yawa na kallon yunkurin yaki da kwararowar hamada matsayin tazo mu jita.
Haka kuma mafi yawan ‘yan Najeriya na sare bishiyoyi, duk da dimbin iskar gas da kasar ke da ita.
Kwamaret Sani Musa Idris, wani dan gwagwarmaya ne mai fafutukar kare muhalli a nan Kano, ya ce akwai bukatar kara zage dantse wajen yin dashen bishiyoyin, domin magance matsalar kwararowar hamada.
Karin labarai:
Majalisar dokokin jiha zata magance matsalolin muhalli
Shin ina makomar matsalar gurbatar muhalli a Jihar Kano
Ko a shekara ta 2010, hukumar raya al’adun Birtaniya da hadin gwiwar hukumar raya gandun daji ta nan Kano, sun gabatar da wani shirin yin dashe a jihar domin magance kwararowar hamada, wanda suka dasa bishiyoyi dubu takwas a wancan lokaci.
Kwararowar hamada dai na daya daga cikin manyan matsalolin da mafi yawan jihohin arewacin Najeriya ke fuskanta.
Sai dai masana sun ce dasa bishiyoyi na daga muhimman matakan da ake dauka domin rage tasirin kwararowar hamadar, a daidai lokacin da ake fama da sauyin yanayi da a yanzu haka ya addabi duniya.
You must be logged in to post a comment Login