Labarai
Yan bindiga sun hallaka mutane biyu ƴan gida ɗaya a yankin Malumfashi

ʼYan bindiga sun hallaka mutane biyu ƴan gida ɗaya a yankin Dansarai da ke Karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wani mazaunin yankin, Abdullahi Naziru Kawo, ya ce ƴan bindigar sun hallaka Shafi’u Sulaiman Dansarai da ƙaninsa
Kawo ya bayyana cewa, mutanen biyu sun rasu bayan samun harbin bindiga yayin harin da ɓarayin daji suka kai garin.
Ya ƙara da cewa, an gudanar da jana’izarsu da ƙarfe 9:00 na safiyar yau Laraba, a gidan Alhaji Hamza Dansarai da ke Karamar Hukumar Malumfashi.
Wani mazaunin yankin, Suleman Iliya, shi ma ya bayyana cewa yankunan Ganzamawa da Dansarai sun fuskanci harin ƴan bindiga a daren jiya Talata.
You must be logged in to post a comment Login