Connect with us

Labarai

Atiku ya barranta kansa da kalaman hadiminsa

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce shirin da yake da shi na tallafawa harkar man fetur ba wai komawa tsarin tallafin man fetur na shigo da shi daga ƙasashen waje ba ne, sai dai tallafi ne da za a mayar da hankali wajen ƙara samar da man fetur a cikin gida da rage tsadar rayuwa.

 

Atiku ya bayyana hakan ne ta hannun babban mataimakinsa na musamman kan yaɗa labarai, Phrank Shaibu, a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

 

Shaibu ya ce bayanin ya zama dole ne bayan wasu kalaman da aka danganta ga Paul Ibe, wanda ya ce gwamnatin Atiku za ta dawo da tallafin man fetur sannan ta cire shi daga baya.

 

Ya bayyana wannan magana a matsayin bayani da ba a ba da izini ba, wanda bai dace da manufar Atiku ba, yana mai cewa masu magana a madadin ɗan takarar ba su da ikon sauya ko ƙirƙirar wata manufa da ɗan takarar bai bayyana ba.

 

A cewar Shaibu, Atiku bai taɓa cewa za a dawo da tsarin tallafin man fetur na shigo da mai daga ƙasashen waje sannan a cire shi a wata ƙayyadaddiyar rana ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!