Connect with us

Labarai

‘Yan bindiga sun sace sarki da matarsa a jihar Kwara

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wani sarki, Oba Salman Aweda, tare da matarsa da wani mutum guda a garin Olayinka da ke karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:40 na daren Asabar, bayan maharan sun kai hari fadar sarkin.

 

Rahotanni sun ce maharan sun rika harbe-harbe domin tsoratar da jama’a kafin su yi awon gaba da wadanda abin ya shafa zuwa wani wuri da ba a sani ba. Mazauna yankin sun bayyana harin a matsayin mai tayar da hankali.

 

Shugaban karamar hukumar Ifelodun, Abdulrasheed Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fara hadin gwiwar aikin ceto tare da jami’an tsaro da ‘yan sa kai. Ya kuma bukaci al’umma su kwantar da hankula tare da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa kokarin kubutar da wadanda aka sace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!