Connect with us

Labarai

Isra’ila ta cigaba da kai hari a Lebanon

Published

on

Sojojin Isra’ila sun ci gaba da rusa gidaje a garin Bint Jbeil da ke kudancin ƙasar Lebanon, a cewar kafar yada labaran gwamnatin ƙasar.

Rahoton ya ce ana sake tayar da bama-bamai domin rusa gidaje a garin, wanda ke kusa da iyakar Israel, kimanin kilomita biyar.

Garin na Bint Jbeil ya kasance wurin da aka gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Isra’ila da kungiyar Hezbollah kafin yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 10 da aka fara aiwatarwa a ranar Alhamis.

Wannan gari yana da muhimmanci a rikicin, domin a nan ne aka yi manyan faɗace-faɗace tun lokacin yaƙin shekara ta 2006.

A baya, ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya bayyana cewa rusa gidajen na daga cikin matakan da ake ɗauka domin kawar da barazanar tsaro a yankin kan iyaka.

Sai dai ministan tsaron Lebanon Michel Menassa ya soki wannan mataki, yana mai cewa hakan na iya janyo tilastawa dubban mutane barin gidajensu tare da lalata kauyuka gaba ɗaya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!