Labarai
’Yan Boko Haram sun kai hari kan ayarin ɗan takarar gwamnan jihar Borno

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa ’yan Boko Haram sun kai hari kan ayarin ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Injiniya Mustapha Gubio.
Kakakin rundunar, ASP Keneth Daso, ya ce harin ya faru ne a kan hanyar Gubio zuwa Kareto da Damasak, a arewacin jihar, yayin da ayarin ke kan hanyarsa daga Damasak zuwa Maiduguri.
Ya ce ’yan ta’addan sun yi wa ayarin kwanton bauna tare da dasa bama-baman IED da kuma harba rokoki, amma jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji, NSCDC, DSS da ’yan banga sun dakile harin.
A cewar ASP Daso, babu asarar rai daga ɓangaren jami’an tsaro ko fararen hula.
Sai dai majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa wata motar sulke ta ’yan sanda da ke cikin ayarin ta samu lahani yayin arangamar.
You must be logged in to post a comment Login