Connect with us

Labarai

INEC za ta fitar da sunayen karshe na ƴan takarar shugaban kasa

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta shirya fitar da jerin sunayen karshe na ƴan takarar shugaban kasa da majalisar kasa da za su fafata a zaben 2027, a ranar Asabar 12 ga Satumba, 2026.

 

Zaben shugaban kasa da na majalisar kasa dai an tsara gudanar da su ne a ranar 16 ga Janairu, 2027.

 

Jerin zai kunshi ƴan takarar shugaban kasa da mataimakansu, da kuma wadanda ke neman kujerun majalisar Dattawa 109 da ta Wakilai 360, wato kujeru 469 gaba daya ke nan.

 

INEC ta ce matakin na cikin jadawalin shirye-shiryen zaɓen, kuma ya yi daidai da tanadin dokar zabe ta 2026, wadda ta tanadi fitar da jerin sunayen karshe akalla kwanaki 60 kafin ranar zabe. 

 

To tuni dai hukumar ta wallafa bayanan ƴan takarar Shugaban Ƙasa domin bai wa jama’a damar duba su tare da gabatar da ƙorafe-ƙorafe kafin kammala jerin sunayen.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!