Labarai
Sokoto – Mutane 5 sun mutu sakamakon harin ‘Yan-bindiga

Rundunar ’yan sandan Jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutane biyar, yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Kebbe.
Harin ya faru ne a yammacin Alhamis a garin Girkau da wasu ƙauyukan da ke yankin, inda mazauna suka ce an kuma yi garkuwa da wasu mutane tare da sace dabbobi.
Kakakin rundunar, DSP Ahmed Rufai, ya ce har yanzu suna tattara bayanai kan adadin mutanen da aka yi garkuwa da su.
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun kai hari ƙauyukan Dukura da Jibga, inda aka kashe mutum ɗaya a kowane wuri, tare da yin garkuwa da wasu mazauna yankin.
Rundunar ’yan sandan ta ce jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login