ilimi
‘Yan damfarar Internet sun sace Naira Miliyan 10 albashin ma’aikata a hukumar JAMB
Masu kutse ta kafar internet sun kutsa cikin shafin hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) tare da sace kudin albashin ma’aikata na wucin gadi da ya kai naira miliyan goma.
Shugaban hukumar ta JAMB farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce, a yanzu hukumar ba ta bukatar dalibai da za su yi rajistar rubuta jarabawar ta JAMB da su yi amfani da adireshin Email din su, saboda gudun kar ya fada hannun masu kutse ta internet.
A cewar sa, hukumar tana ci gaba da aiki tukuru don ganin ta dakile matsalolin da ya janyo masu kutsen su ka samu damar shiga shafin hukumar tare da karkatar da kudaden ma’aikatan zuwa wani asusu na daban.
Sai dai ya ce, bayan da aka gudanar da bincike, an samu nasarar kama wani da ake zargi yana da masaniya kan batun mai suna Sahabi Zubairu mazaunin garin Takum da ke jihar Taraba.
You must be logged in to post a comment Login