Labarai
Yan kasuwa sun fara mayar da martani kan kalaman ministan man fetur
Gamayyar kungiyoyin yan kasuwa a Najeriya sun fara mayar da martani karamin ministan manfetur Timipre Sylva kan furucin da yayi cewa yan Najeriya su shirya fuskantar karin farashin man fetur.
Shugaban gamayyar kungiyoyin yan kasuwar Quadri Olaleye ya ce a kullum gwamnati kanyi mazari wajen kara farashin man fetur, ba tare da yin la’akari da halin matsin rayuwar da yan kasar ke ciki ba
Ya ce sam-sam abinda gwamnatin tarayya keyi bai da ceba, adon haka kamata yayi ta mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da kuma fatara
Haka nan ma kungiyar masu sarrafa kayayyaki ta Najeriya da cibiyar cinikayya ta Legas sun nemi gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kudaden da ta ke samu daga bangaren manfetur wajen magance wadannan matsaloli
You must be logged in to post a comment Login