Kiwon Lafiya
Yan Najeriya 490 ne aka dawo da su daga kasar Libya
Akalla ‘yan-Najeriya 490 ne aka dawo da su gida daga kasar Libya a yammacin jiya Lahadi bayan da jirginsu ya sauka garin Fatakwal na Jihar Rivers.
Mutanen na daga cikin ‘yan-Najeriya 5,027 da ake sa-ran dawo da su gida Najeriya sakamakon makalewa da suka yi a can Libya suna fuskantar cin zarafi da muzgunawa a hannun hukumomin kasar da kuma masu bautar da jama’a.
Ministan harkokin wajen kasar nan Geofrrey Onyeama ya ce gwamnatin tarayya za ta basu horo na musamman tare da tabbatar da cewa sun samu abin yi domin komawa cikin al’ummarsu cikin kyakkyawan yanayi.
Ministan ya shaida cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin tanadar kudaden domin dawo da mutanen cikin hayyacinsu.
A nasa bangaren babban kwanturolan hukumar kula da shige-da-fice ta kasa Muhammad Babandede, cewa ya yi ‘yan-Najeriya na da ‘yancin tafiye-tafiye zuwa ko ina a Duniya kuma akwai ‘yan-Najeriyan da ke kasar Libya dauke da cikakkun takardu, a don haka ya bukaci masu yin tafiye-tafiyen da su rinka yi ta hanyar bin dokoki da ka’idoji.