Coronavirus
‘Yan Najeriya 500 sun dawo gida daga daular larabawa
Gwamnatin tarayya ta ce, ta dawo ‘yan-kasar nan mazauna hadaddiyar daular Larabawa su dari biyar da Casa’in ajiya Talata.
Ministan zirga-zirgar kasashen waje Geoffrey Onyema ne ya bayyana hakan ta cikin rahoton da ya wallafa a shafin sa na Twitter a yammacin jiya.
Geoffrey Onyema ya ce dari uku da biyar daga cikin matafiyan an dawo da su ta jirgin Emirate Airline.
Sanarwar ta kuma ce, matafiyan sun sauka a filin jirgin saman Nmandi Azikiwe da ke birnin tarayya Abuja.
Onyema ya ce, ce ragowar matafiyan guda dari biyu da sittin da daya sun sauka a kasar nan da misalin karfe daya na rana yayin da guda dari uku da ashirin da tara suka sauka da misalin karfe daya da rabi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke jihar Lagos.
Sanarwar ta ce dukkanin matafiyan za su killace kan su na tsawon mako biyu don tabbar da ingancin lafiyar su.
Onyema ya bayyana cewa wannan shine karo na biyar da gwamnatin tarayya ta dawo da yan kasar da ke wasu kasashen tun bayan bullar annobar corona.
You must be logged in to post a comment Login