Labarai
‘Yan Najeriya su guji auren kwangila da ‘yan ketare – Babandede
Hukumar kula da Shige da fice ta kasa ta gargadi yan Najeriya da su guji yin auren kwangila daga kasashen ketare.
Kwanturola Janar na hukumar ta kasa Muhammad Babandede ne yayi gargadin, a wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja jiya Laraba.
Yin hakan babban laifi ne, saboda ya hana gwamnatin tarayya samun kudin shiga ta bangaren haraji da kuma mallakar takardun izinin zama ga bakin.
Gargadin ya zama dole, saboda hukumar ta lura cewa a shekarar 2020, yawan baki da suka samu takardun izinin zama a Najeriya ya ninka har sau uku.
Babandede ya bayyana cewa hukumar ta cafke wani dan kasar China da wasu yan kasar Masar da dama wadanda suka yi amfani da auren jabu don neman izinin zama a kasar nan.
Babandede ya ce daga yanzu, ya zama dole ga duk mai son zama a kasar nan ya rika sabunta takardun izinin zama, wanda hukumar su zata hada kai da hukumar tara haraji ta kasa don tabbatar da bakin haure na biyan kudaden haraji.
You must be logged in to post a comment Login