Connect with us

Labarai

Yan sanda a Jihar Rivers sun kama masu garkuwa da mutane

Published

on

‘Yan sanda a Jihar Rivers sun kama wasu manyan masu garkuwa da mutan guda uku tare da ceto wasu da aka sace. An kama su ne yayin da suke ƙoƙarin sace wani mutum da suka yaudara daga Jihar Anambra da sunan za su ba shi aikin gyaran ciki (interior decoration). Rundunar ta bayyana cewa wannan nasara na daga cikin kokarin da suke yi na dakile laifuka a jihar.

 

Bincike ya nuna cewa waɗannan masu laifin suna amfani da kafafen sada zumunta kamar WhatsApp, Facebook, X da Tinder wajen yaudarar mutane. Suna amfani da hotunan manyan mutane domin samun amincewa daga wurin waɗanda suke son yaudara, sannan su jawo su zuwa jihar kafin su yi garkuwa da su.

 

Wadanda aka kama sun amsa laifukan da suka hada da wasu sace-sacen mutane a baya, yayin da jagoran kungiyar ya tsere. Rundunar ‘yan sanda ta shawarci jama’a da su rika yin taka-tsantsan da mutane da ba su sani ba a intanet, su tabbatar da sahihancin duk wata tayin aiki, kuma su sanar da ‘yan uwa kafin su hadu da sabbin mutane.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!