Labarai
Paparoma Leo ya karyata labarin takun saka da Trump

Shugaban darikar Katolika Paparoma Leo XIV ya karyata rade-radin cewa yana takun saka da shugaban Amurka Donald Trump. Ya ce bai da niyyar shiga wata muhawara da Trump, kuma maganganun da ya yi game da “azzalumai da ke lalata duniya” an rubuta su tun kafin Trump ya yi masa suka.
Ya bayyana cewa wasu sun fassara kalamansa ba daidai ba, musamman kafafen yaɗa labarai na Amurka da suka ɗauka kamar yana nufin Trump. Amma shi ya ce ba haka ba ne, domin manufarsa ita ce yada saƙon zaman lafiya, ba rikici ba.
A baya dai Trump ya soki Paparoman, yana cewa bai gamsu da shi ba, kuma ya zarge shi da sassaucin ra’ayi kan batun Iran da makaman nukiliya. Duk da haka, Paparoman ya nuna ba ya son wannan ya zama wata muhawara tsakaninsu.
You must be logged in to post a comment Login