ilimi
Malaman makaranta a Abuja za su tsunduma yajin aiki

Reshen kungiyar malaman makaranta ta NUT na Abuja Babban Birnin Tarayyar Nijeriya ya umarci malaman makarantun firamare da sakandare a dukkan gundumomi shida da ke yankin da su shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026.
Shugaban kungiyar Comr Abdullahi Mohammed Shafas, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai bayan wani taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na reshen jiha (SWEC) da aka gudanar a Teachers House da ke Gwagwalada.
Ya ce sun dauki matakin ne saboda rashin fitar da kuma aiwatar da rahoton da ya shafi hakkokin da malaman ke bi wanda gwamnatin FCT ta kasa kammalawa.
You must be logged in to post a comment Login