Connect with us

Labarai

Yan sanda sun gayyaci Nasir El-Rufai

Published

on

Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Kaduna ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, domin amsa tambayoyi kan zargin hada baki wajen aikata laifi da tayar da hargitsi da barna da kuma jikkata wasu mutane.

Wannan kira na zuwa ne daga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar, karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Zubairu Abdullahi.

Haka kuma, takardar gayyatar ta nuna cewa wasu shugabannin jam’iyyar, ADC, a jihar, ciki har da shugaban jam’iyyar na Arewa maso Yamma, Ja’afaru Sani, suma an bukaci su bayyana gaban ‘yan sanda don fuskantar tambayoyi.

A cewar rundunar, an gayyaci El-Rufai tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar guda shida da suka hada da: Bashir Saidu, Ja’afaru Sani, Ubaidullah Mohammed, wanda aka fi sani da Mikiya 30, Nasiru Maikano, Aminu Abita, da kuma Ahmed Rufa’i Hussaini..

Takardar gayyatar ta ce rahoton da aka samu daga wasu masu korafi a ranar takwas ga watan Satumba, ya sa ake bukatar wadanda ake zargin su bayyana domin fayyace matsayar su kan tuhumar da ake musu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!