Connect with us

Labarai

Yan Sanda sun kama bata gari 262 tare da kubutar da mutane 27 da aka sace

Published

on

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce, ta kama mutane 262 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da kubutar da mutane 27 da aka yi garkuwa da su, cikin makon da ya gabata.

 

Rundunar ta ce an gudanar da samamen ne tsakanin 5 zuwa 11 ga watan Satumba, inda aka kwato bindigogi 34, harsasai 375 da motoci 11. Haka kuma, an hallaka wasu ’yan bindiga 11 yayin arangama da jami’an tsaro.

 

Mai magana rundunar, Ani Iniedu, ya ce, ta bayyana hakan a cikin makon ta na mai cewa, an samu rahotannin kisan kai 50, fashi da makami 28, garkuwa da mutane 27, ta’addanci biyar da kuma hare-haren ’yan bindiga 22 a sassa daban-daban na kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!