Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun kuɓutar da mutane uku da aka yi garkuwa da su, bayan kai samame maboyar da ake zargin ’yan bindiga ne suka kafa a ƙaramar hukumar Makarfi.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce an kai samamen ne a ranar Alhamis, bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin wasu da ake zargi da aikata laifuka a yankin Gidan Mijin Gwaggo da Durum.
A cewar kakakin rundunar, Mansir Hassan, kwamishinan ’yan sanda Rabiu Muhammad ne ya umarci jami’an rundunar Makarfi, tare da ’yan banga, su kai farmaki wurin.
Ya ce da jami’an suka isa wurin, waɗanda ake zargin ’yan bindigar ne suka bude musu wuta, lamarin da ya haifar da musayar wuta mai tsanani.
Rundunar ta ce hakan ya tilasta wa ’yan bindigar tserewa zuwa cikin daji, inda ake zargin wasu daga cikinsu sun samu raunukan harbin bindiga.
Bayan haka, jami’an tsaron sun binciki wani gida mallakin wani mai suna Yakubu Sule, inda suka gano cewa an yi amfani da gidan a matsayin maboyar ’yan bindigar.
Rundunar ta ce mutane ukun da aka yi garkuwa da su na daga cikin waɗanda aka tsare a gidan, kuma an kuɓutar da su ba tare da wani rauni ba.
Daga cikin waɗanda aka kuɓutar akwai Alhaji Hamza Gimi, tare da wasu mutum biyu, kuma an sake haɗa su da iyalansu.
Jami’an tsaro sun kuma kwato wani babur kirar Boxer da ake zargin masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da shi, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafke waɗanda suka tsere.
You must be logged in to post a comment Login