Labarai
Yan sanda sun sake kama matasa 57 da ake zargi da fasa shaguna a Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, ta sake cafke wasu matasa su 57 da ta ke zarginsu da laifin hada kai da yin sata ta hanyar fasa shagunan mutane.
Ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar da safiyar yau Juma’a.
Ya ce, an samu nasarar kama matasan ne dauke da wasu daga cikin kayayyakin mutane da ake zargin na sata ne da suka sato su daga cikin irin wuraren da gwamnatin jihar Kano ke rushewa da gwamnatin ta ce an gina su ne ba bisa ka’ida ba.
Haka zalika rundunar ta ce, bayan wadannan matasa da ta sake cafkewa, ta gurfanar da kimanin matasa 49 a gaban kotunan majistiri da ke Normal Sland kan zargin hada kai, sata da kuma Balla shagunan mutane.
Haka kuma rundunar ta sake gurfanarda mutane 57 a gaban kotunan na majistiri da makamancin laifukan da ake zargin matasan da aikatawa dauke da abunda suke karya shagunan jama’a, wanda a yanzu yawansu ya kai mutane dari da shida.
Haka kuma, rundunar yan sandan ta jihar Kano, ta shawarci matasa da su guji sanya kansu cikin duk wani abu da zai iya jefa su cikin mawuyacin hali domin inganta rayuwarsu.
Rahoton; Abdulkarim Muhaammad Tukuntawa
You must be logged in to post a comment Login