Labarai
Yan Sanda sun tabbatar da rasuwaShiekh Yahaya Masussuka

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka, wanda ake zargin wasu ’yan bindiga dake kan babur sun harbe shi a kofar gidansa da ke garin Dutsinma a daren Litinin, wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ƙofar gidan malamin, lokacin da maharan su ka buɗe masa wuta tare da wani amininsa.
Bayan harin, an garzaya da su zuwa Asibitin Dutsin-Ma domin samun agajin gaggawa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.
Ya zuwa yanzu, ba a samu cikakken bayani kan dalilin kisan ko waɗanda suka aikata shi ba.
Lamarin ya jefa al’ummar Dutsin-Ma cikin alhini, musamman mabiyan Sheikh Yahaya Masussuka da sauran waɗanda suka san shi a cika da wajen Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login