Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya na shirin samar da cibiyoyin kula da masu cutar Ebola

Published

on

Gwamnatin Tarayya na shirin samar da cibiyoyin kula da masu cutar Ebola a jihohin dake fadin kasar nan.

 

Wannan dai na zuwa ne sakamakon samun mutane 53 da ake zargin sunyi mu’amula da mutumin da ya kamu da cutar ta Ebola a fadin kasar nan.

 

Haka kuma, gwamnatin ta ce, za ta samar da kayayyakin aiki a dukkan cibiyoyin da zata samar a jihohin.

 

Wannan mataki na faruwa ne yayin da hukumar Kula da Cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta amince da biyan kuɗin tallafin gaggawa na naira dubu ɗari ga kowane mutum a mako, domin taimaka wa waɗanda aka killace ko aka keɓe saboda yiwuwar kamuwa da cutar Ebola.

 

Babban Daraktan hukumar, Dokta Jide Idris, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.

 

Ya kuma ce an samar da tallafin ne domin rage wa mutanen nauyin kuɗin abinci, masauki da kula da iyalansu, tare da ba su damar bin ƙa’idojin sa ido kan lafiyarsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!