Labarai
Yan sandan Imo sun gano sansanin da aka tsare yan hidimar kasa 19 da aka sace

Yan sanda a jihar Imo sun ce sun gano wani sansani da ake tsare da aƙalla matasa 19 masu yi wa ƙasa hidima da ƴanbindiga suka sace a baya-bayan nan.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Audu Bosso, ya ce jirage marasa matuƙa sun taimaka wajen gano sansanin, amma jami’an tsaro ba su kai ga isa wajen ba saboda ana kyautata zaton an dasa abubuwan fashewa a zagayen wajen.
Da yake magana da manema labarai, Bosso ya ce sun shiga daji, sun bi sawunsu har zuwa wani wuri.
Sai dai ya ce amma a lokacin ba mu iya kutsawa zuwa wurin da bayananmu suka nuna mana cewa suna can ba.
Ya ce binciken da aka yi da jirgi marar matuƙi ya tabbatar da inda sansanin yake.
You must be logged in to post a comment Login