Labarai
Yari ya bukaci yan Arewa su guji amfani da yawan jama’a wajen kalubalantar raba madafun iko

Daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Sanata Abdul’Aziz Yari Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Arewa da ka da su yi amfani da yawan al’ummar yankin wajen kalubalantar tsarin raba madafun iko.
Haka kuma Abdul’aziz Yari, ya ce, ya kamata Arewa ta mutunta fahimtar siyasar da ta kai ga fitowar Shugaba Bola Tinubu daga Kudu a shekarar 2023, tare da ba shi damar kammala wa’adinsa na shekaru takwas.
Da ya ke magana a gidan gwamnatin Kano bayan ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, Yari ya ce Arewa ta rike shugabancin Najeriya na tsawon shekaru, kafin a mika mulki ga Kudu.
Ya ce, idan Tinubu ya kammala wa’adinsa a shekarar 2031, ya kamata shugabancin kasar ya koma Arewa, yana mai cewa tsarin raba madafun iko na da muhimmanci wajen tabbatar da hadin kan kasa.
You must be logged in to post a comment Login