Labarai
Shugaba Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin sojin saman

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan fasinjoji da ma’aikata 7 da suka rasu sanadin hatsarin jirgin sojin saman Najeriya a jihar Ondo.
A sanarwar da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya kaɗu da labarin hatsarin jirgin da ya yi ajalin dukkan mutum 32 da ke ciki da suka hada da fasinjoji 25 da ma’aikata 7.
Ya mika sakon ta’aziyya ga Babban hafsan sojin sama Air Marshal Sunday Kelvin Aneke da dukkan ma’aikatan maza da mata na rundunar sojin sama ta kasa.
Tinubu ya ce wannan ranar baƙin ciki ce ba ga sojoji ba har ga ƴan Najeriya baki ɗaya, ya ce sojoji na sadaukar da rayukansu domin kare ƴan ƙasa.
Ya kuma bada umarnin gudanar da binciken gaggawa kan musabbabin haɗarin jirgin, da lalubo hanyar magance aukuwar hakan nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login