Connect with us

Labarai

Iyalan matasan NYSC da aka sace sun bukaci dauki daga mahukunta

Published

on

Iyalan  matasan nan 20 da aka sace a lokacin da suke tafiya sansanin NYSC a jihar Oyo na cigaba da fargaba bayan  da masu garkuwar sun ba su wa’adin sa’o’i 24 su biya kudin fansa na naira biliyan daya domin a sakin ‘ya’yan nasu.

Rahotanni sun ce matasan, waɗanda suka fito daga Jihar Oyo, an sace su ne a ranar Alhamis yayin da suke tafiya daga Ibadan zuwa sansanin horas da masu yi wa kasa hidima a Jihar Imo. Masu garkuwar sun bukaci naira miliyan 50 ga kowane mutum guda.

Iyalan matasan sun bayyana hakan ne yayin da suka kai ziyara ga Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, inda suka roƙe shi da jami’an tsaro su taimaka wajen ceto ‘ya’yansu. 

A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sandan Jihar Oyo, Olugbenga Abimbola, ya ce ya tuntubi takwaransa na Jihar Imo, wanda ya tabbatar masa da cewa ana kokarin ceto matasan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!