Labarai
’Yan Sandan a Benue sun kubutar mutane 5 cikin fasinjoji 14 bayan garkuwa da su

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue ta kubutar mutane biyar daga cikin fasinjoji 14 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Ohimini ta jihar.
Rundunar ta bayyana cewa, an yi garkuwa da fasinjojin ne a daren Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, yayin da suke tafiya daga Enugu zuwa Abuja a motar haya ta hanyar Ankpechi zuwa Omutele.
’Yan sanda sun ce an yi musayar wuta da waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutanen ne yayin aikin ceto, inda aka ceto mutane biyar ciki har da yaro mai shekara huɗu, yayin da mutum ɗaya ya samu raunin harbin bindiga.
Rundunar ta ce sauran mutane tara na hannun masu garkuwa da su, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin ceto su.
You must be logged in to post a comment Login