Labarai
Atiku ya shigar da kara kotu kan ta hana Tinubu takara a zaben 2027

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar, ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana neman a hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Atiku ya ɗauki wannan mataki ne bisa zargin cewa an samu sabanin bayanai da kuma takaddamar sahihancin takardar sallamar hukumar Bautar kasa ta NYSC da ake dangantawa da Shugaba Tinubu.
A cikin ƙarar, Atiku ya nemi kotu ta binciki takardun da Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, musamman bayanan da suka shafi takardar NYSC.
Ya kuma nemi kotu ta yi amfani da tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da ya shafi rashin cancantar wanda aka tabbatar da cewa ya gabatar da takardar bogi wajen neman takarar shugaban ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login