Connect with us

Labarai

Ana zargin jam’iyyun APC da Accord da sayen ƙuri’u a zaben Osun

Published

on

Rahotanni daga jihar Osun na cewa jam’iyyun APC da Accord na fuskantar zargin sayen ƙuri’u gabanin zaɓen gwamnan jihar da ake gudanarwa yau Asabar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu masu zaɓe sun ce wakilan jam’iyyun sun rika bai wa mutane kuɗi tsakanin naira dubu 10 zuwa dubu 20, tare da tattara bayanan asusun bankinsu domin biyan wasu bayan zaɓe.

A wasu wurare kamar Ilesa, Osogbo, Iwo, Ila da Ile-Ife, an zargi APC da bayar da kuɗi daban-daban, yayin da Accord ma ke rarraba kuɗi ga masu zaɓe.

Wasu daga cikin masu cin gajiyar kuɗin sun kuma ce an nemi su rantse cewa za su zaɓi ɗan takarar jam’iyyar da ta ba su kuɗin.

A gefe guda, ’yan sanda sun gargadi ’yan siyasa da masu zaɓe kan saye ko sayar da ƙuri’a, inda suka ce za su kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a hakan.

Rahoton ya kuma ce an samu kashe-kashen mutane a wasu sassan jihar cikin makon da ya gabata, lamarin da ya sa aka tura jami’an tsaro, ciki har da sojoji, zuwa wasu wuraren da ake ganin suna da hatsari.

Ƙungiyar YIAGA Africa ta bayyana damuwa kan yawan zargin sayen ƙuri’u da tashin hankalin siyasa, tana cewa hakan na iya sanya a yi shakku kan sahihancin sakamakon zaɓen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!