Labarai
Yan siyasa da rashin kyakkyawan shugabanci ne ke haddasa matsaloli a Najeriya- Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce ‘yan siyasa da rashin kyakkyawan shugabanci ne ke haddasa manyan matsalolin da kasar nan ke fuskanta.
Obi ya bayyana hakan ne, yayin da yake jawabi ga manema labarai dan gane da matsalolin da siyasar kasar nan ke ciki.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce babu wata matsala ta asali da Najeriya ke da ita, illa rashin ingantaccen shugabanci.
Ya kuma bukaci jama’ar da suka halarci taron su rika sanya ‘yan siyasa cikin addu’o’insu.
You must be logged in to post a comment Login