Labarai
An yi jana’izar marigayi Engr. Kamal Muhammad Jamil Fagge

Da safiyar yau Talata ne aka yi jana’izar Injiniya Kamal Muhammad Jamil Fagge, wanda ya kasance guda daga cikin ma’aikacin Freedom Radio Kano.
A wayewar garin yau Allah ya yi wa marigayin rasuwa sakamakon gajeruwar rashin lafiya.
Marigayin dai na aiki da sashen Injiniyoyi, sai na shirye-shirye da ya ke gabatar da labaran wasanni.
Yayin zantawar Freedom Radio, da mai dakin sa Nafisa Jibrin Hassan, cikin alhini ta bayyana zaman da su kayi da marigayin da ta ce ba za ta taba mantawa da shi ba sakamakon irin kulawarsa ga iyalansa.
Marigayi Kamalu, ya rasu ya bar mata biyu da yara Maza biyu, da kuma ‘yan uwa da dama.
You must be logged in to post a comment Login